Isa ga babban shafi
Zaben Kenya

Madugun 'yan adawar Kenya ya yi fintinkau a zaben kasar

Yayin da ake dakon Hukumar Zaben Kenya ta IEBC ta sanar da sakamakon zaben shugabancin kasar da ya gudana a jiya Talata, babbar jaridar kasar ta Nation ta wallafa alkaluman wucen-gadi da ta tattara da ke nuna cewa, madugun 'yan adawar kasar Raila Odinga na kan gaba wajen samun yawan kuri'u, inda ya yi wa babban abokin takararsa kuma mataimakin shugaban kasa William Ruto fintikau.

Raila Odinga
Raila Odinga © Raila Odinga twitter
Talla

Ga jadawalin sakam,akon da jaridar ta wallafa

Raila Odinga- 49.81%

4,016,525 ( Kuri'u)

William Ruto- 49.53%

3,994,013 ( Kuri'u)

George Wajackoyah- 0.44%

35,402 ( Kuri'u)

David Waihiga- 0.23%

18,460 ( Kuri'u).

Kowane lokaci daga yanzu ake sa ran Hukumar Zaben Kasar ta fitar da na ta sakamakon, yayin da al'ummaar kasar suka kagu su san wanda zai gaji shugaba mai shirin barin gado, Uhuru Kenyatta.

Ruto da Odinga, dukkaninsu sun yi alkawarin rungumar kaddara kan yadda za ta kaya, amma duk da haka ‘yan kasar ta Kenya sun gaza mancewa da tashe-tashen hankulan da suka a gani a zabukan shekarun baya da suka gabata.

Jami’an Hukumar Zaben Kasar ta IEBC da ke shan matsin lamba, sun shafe tsawon dare suna ta kidayar kuri’u karkashin kulawar masu sanya ido, kuma duk irin jinkirin da za a samu na fitar da sakamakon zaben, babu shakka ba zai wuce ranar 16 ga wannan wata na Agusta ba.

Shugaban Hukumar Zaben, Wafula Chebukati ya roki ‘yan Kenya da su ci gaba da hakuri duk da cewa, sun kagu su ga an fitar da sakamakon zaben cikin gaggawa domin kauce wa zarge-zargen tafka magudi kamar yadda aka gani a zabukan baya.

A jiya Talata ne jama’ar Kenya da suka yi dogayen layuka tun da asuba, suka kada kuri’unsu a zabuka shida da suka hada da na shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci, ‘yan majalisa da na wakilan mata har ma da na kananan hukumomi.

Koda yake a wannan karo,  an samu karancin fitowar masu kada kuri’a, idan aka kwatanta da zabukan da suka gabata

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.