Isa ga babban shafi

Atiku ya gana da Wike kan rikicin jam'iyyar PDP

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas sun gana a Abuja, babban birnin kasar.

Atiku Abubakar tare da Nyesom Wike
Atiku Abubakar tare da Nyesom Wike © Daily Trust
Talla

Mutanen biyu da ke fafatawa tun bayan zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar PDP sun gana a gidan Farfesa Jerry Gana a ranar Alhamis.

Atiku ya kayar da Wike a zaben fidda gwani, amma Gwamnan Ribas ya nuna sha’awarsa ta zama mataimakin dan takarar Shugaban kasar, amma Atikun ya zabi Gwamna Ifeanyi Okowa na Jihar Delta a matsayin wanda za su tafi tare.

Hakan dai ya kara ta’azzara rikicin PDP yayin da Wike ke takun-saka da shugabannin jam’iyyar APC mai mulkin kasar.

Takun sakar da ta kunno kai tsakanin mutanen biyu, rahotanni sun ce hakan ya kawo tsaikon kafa kwamitin yakin neman zaben Atiku.

Sai dai kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP ya gudanar da tattaunawa kan batun tsakanin Atiku da Wike inda suka yanke shawarar sasanta mutanen biyu.

Bayan taron na ranar Laraba da kwamitin ya gudanar, Sanata Abdul Ningi, wato mukaddashin sakataren kwamitin, ya shaida wa manema labarai cewa mambobin kwamitin za su warware matsalar tare da baiwa jam’iyyar damar gabatar da ra’ayin bai daya kan babban zaben kasar da ke tafe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.