Isa ga babban shafi

Ana jiran sakamakon zaben majalisar dokoki, kananan hukumomi a Congo Brazaville

Ana dakon sakamakon zaben 'yan majalisar dokoki da na kananan hukumomi da aka gudanar Jiya Lahadi a kasar Congo Brazzaville, wanda da alama jam'iyya mai mulki za ta ci gaba da rike rinjayen majalisar dokokin kasar, ko da yake wasu bangarorin  ‘yan adawa sun kaurace wa zaben.

Shugaban Congo Brazaville Sassou Nguesso.
Shugaban Congo Brazaville Sassou Nguesso. © AP - Francois Mori
Talla

Zaben na ranar Lahadi, wanda ke zama zakaran gwajin dafi ga zaben shugaban kasa dake tafe, ya dan samu jikirin akalla sa’a guda kan lokacin bude runfunan zabe, yayin da aka samu karin fitowar masu kada kuri’u.

A makarantar Nkeoua Joseph da ke mazabar Bacongo a babban birnin kasar, inda 'yan takara bakwai ke fafatawa, sai bayan karfe 8 agagon kasar mutun na farko ya kada kuri'arsa, maimakon karfe 7 kamar yadda aka tsara.

Hukumar zaben Congo Brazzaville ta ce sama da 'yan takara dubu 2 ke neman zuwa Majalisar Dokokin mai kujeru 151.

Yanzu haka jam'iyyar Labour Party ta shugaban kasar Denis Sassou Nguesso ce ke da rinjaye a majalisar da wakilai 101 cikin kujeru 151.

Nguesso, mai shekaru 78, tsohon sojan sama, ya shafe shekaru 37 a kan karagar mulkin Congo.

Kansilolin da aka zaba a zaben na Lahadi, su zasu nada Sanatoci 72 a karon farko zuwa zauren Majalisar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.