Isa ga babban shafi

An caccaki yadda gwamnatocin yankin Sahel ke tinkarar matsalar tsaro

Wata kungiya da ke sanya idanu kan yadda al’amurran tsaro ke tafiya a kasashen yankin Sahel, ta yi tir da yadda gwamnatocin kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso ke tunkarar harkokin tsaro a kasashen su.

Wasu Sojin kasashen Sahel.
Wasu Sojin kasashen Sahel. RFI / Anthony Fouchard
Talla

Kungiyar ta cikin wani kundin bincike da ta fitar, ta ce abin kunya ne yadda kasashen ke tunkarar harkokin tsaro, yayin da karara yake nuna ba da gaske suke yi ba, a dai-dai lokacin da rayukan al’ummar su ke ci gaba da salwanta.

Harkokin tsaro ya tabarbare a wadannan kasashe, tun daga tushe, kuma karara yake shugabannin kasashen basa wani hobbasa na azo a gani wajen kawo karshen masu rike da makamai da sunan jihadi a cewar kungiyar.

Ta cikin kundin binciken, kungiyar ta kuma kara da cewa harkokin kasuwanci, ilimi da kuma lafiya sun lalace a wadannan kasashe, saboda yadda ‘yan ta’adda ke kaiwa kasuwanni makarantu da kuma asibitoci hari kusan kowacce rana.

Kungiyar ta kuma kara da cewa, kididdigar ta na nuni da cewa kowacce rana fararen hula 8 na rasa rayukan su a hannun ‘yan ta’adda tun daga watan Afrilun bara zuwa watan Maris din da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.