Isa ga babban shafi

Sarkin Belgium na ziyarar sasanci a Jamhuriyar Demokradiyar Kwango

Sarkin Belgium Philippe ya isa birnin Kinshasa na Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango da yammacin Talata,  ziyarar irinta ta farko a wani mataki sasantawa tsakaninta da kasar da ta yi wa mulkin mallaka.

Sarki Philip na Belgium da uwargidansa tare da shugaban kasar Jamhuriyar Demokradiyar Kwango Felix Tshishekedi a Kinshasa.2022-06-07
Sarki Philip na Belgium da uwargidansa tare da shugaban kasar Jamhuriyar Demokradiyar Kwango Felix Tshishekedi a Kinshasa.2022-06-07 © Presidence du RDC
Talla

Shugaban kasar Félix Tshisekedi, da mai dakinsa ​​da wasu manyan jami’an gwamnati da siyasa daban-daban ne suka hallara a filin jirgin saman Kinshasa domin tarbar sarki Phillipe da uwargidansa ​​Mathilde da tawagar gwamnatin Belgium.

Sarki Philip na Belgium yayin ziyara a Jamhuriyar Demokradiyar Kwango 07/06/22
Sarki Philip na Belgium yayin ziyara a Jamhuriyar Demokradiyar Kwango 07/06/22 © Presidence du RDC

Wannan ziyarar masarautar Belgium itace ta farko, tun bayan wacce Mahaifin Philipe wato sarki Albert na ii ya kai a shekarar 2010.

Dage ziyarar

Sau biyu ake dage ziyarar sarki Phillips zuwa Jamhuriyar Demokradiyar Kwango, an dage ziyarar farko a shekarar 2020 saboda barkewar annobar korona, sannan a farkon wannan shekara saboda yakin Rasha da Ukraine.

Sarki Philip na Belgium yayin ziyara a Jamhuriyar Demokradiyar Kwango 07/06/22
Sarki Philip na Belgium yayin ziyara a Jamhuriyar Demokradiyar Kwango 07/06/22 © Presidence du RDC

Yayin bukin cika shekaru 60 da samun yanci da jamhuriyar Demokrdiyar Kwango shekaru biyu da suka gabata, masarautar Belgium da ta yi mata mulkin mallaka ta aikewa shugaba Felix Tshisekedi da al’ummar kasar wasika, inda a ciki suka nuna nadama kan rauni da sukayi mata lokacin mulkin mallaka.

Hakuri

Sarkin Phillipe wanda ke mulki tun shekarar 2013, ya yi nadama da "ayyukan cin zarafi da rashin tausayi" da aka yi a lokacin mulkin kakansa Leopold na II, wanda ya mayar da Kongo tamkar dukiyarsa  a shekarun (1885-1908).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.