Zanga-zangar nuna goyon baya ga Christian Marc Kabore
A Burkina Faso, dubban magoya bayan tsohon Shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore ne suka fito don nuna damuwar su ganin ci gaba da tsare tsohon shugaba da majalisar sojin kasar ke yi yanzu haka.
Wallafawa ranar:
Magoya bayan tsohon Shugaban sun gudanar da zanga-zangar lumanar ce a birnin Ouagadougou.
Yayin jawabi ga manema labarai sun gargadi majalisar sojin kasar da ta gaggauta kawo karshen tsare tsohon Shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore da aka kifar ranar 24 ga watan janairun shekarar nan, mudin hakan ba ta samu ba to za su fadada wanan zanga-zanga zuwa sauren yankunan kasar ta Burkina Faso 45.
Kungiyar kasashen Yammacin Afrika ta Ecowas ta shiga tattaunawa da majalisar sojin kasar ta Burkina Faso,na ganin lamura sun daidata,tun bayan juyin mulkin watan janairu,ba tareda cimma wani muhimin sauyi ba yanzu haka
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu