Isa ga babban shafi
AFIRKA-NOMA

Afirka bata bukatar agajin abinci daga kasashen duniya - Adeshina

Bankin raya kasashen Afirka na AfDB ya amince da ware Dala biliyan guda da rabi a matsayin agajin gaggawa domin taimakawa jama’ar dake nahiyar wajen shawo kan matsalar karancin abinci sakamakon yakin kasar Ukraine.

Shugaban Bankin Raya kasashen Afirka Akinwumi Adeshina
Shugaban Bankin Raya kasashen Afirka Akinwumi Adeshina AFP
Talla

Shugaban Bankin Akinwumi Adeshina ya sanar da daukar matakin inda yake cewa za’a yi amfani da kudaden ne wajen taimakawa kasashen dake nahiyar samar da abincin da ake bukata.

Adeshina yace akalla manoma miliyan 20 dake Afirka zasu amfana daga wannan shiri domin noma tan miliyan 30 na nauyin abinci iri iri da suka hada da alkama da masara da waken soya wadanda ake sayowa daga Ukraine.

Shugaban bankin yace a karkashin wannan shirin ana bukatar noma tan miliyan 38 na abincin da ya kunshi tan miliyan 11 na alkama da tan miliyan 18 na masara da tan miliyan 6 na shinkafa da kuma tan miliyan biyu da rabi na waken soya.

Adeshina yace agajin abinci daga kasashen duniya ba zai ciyar da nahiyar Afirka ba, kuma Afirka bata bukatar yawo da kokon bara, sai dai samun ingantaccen iri da injinan noma da zasu bada damar samar da abincin da ake bukata.

Shugaban Bankin yace Afirka za tayi alfaharin ciyar da kan ta ta kowacce fuska, saboda haka babu dalilin yawo da kokon bara ana neman taimakon abincin da za’a ciyar da jama’a.

Adeshina ya kuma bayyana shirin samar da takin zamani da iri da kuma taimakawa manoma wajen girbi baya ga rancen kudade da kuma tallafi wajen bunkasa noman.

Bankin raya kasashen Afirka yace muddin aka gaza wajen shawo kan wannan matsala, ana iya samun gibin abincin da ya kai kashi 20, kuma nahiyar na iya asarar da ta kai Dala biliyan 11.

Yanzu haka farashin abinci a Afirka ya tashi da kashi 45 sakamakon mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine, yayin da farashin takin zamani ya tashi da kashi 300 abinda ke nuna fargabar samun karancin sa a nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.