Shekaru 41 da rasuwar Bob Marley, mawakin Rasta
Robert Nesta da aka fi sani da sunan Bob Marley, an haife shi ne ranar 6 ga watan Fabrairu shekarar 1945 a Nine Milesa kasar Jamaica.Ya dai gudanar da aikace-aikace ka fi ya samu kansa a duniyar mawaka.Ya shiga duniyar mawaka a shekara ta 1962 ya na mai shekaru 17.
Wallafawa ranar:
A shekara ta 1963 ne ya kafa kungiyar The Wailers tareda taimako Bonny Wailley da Peter Tosh.
Daya daga cikin wakokin su na lokacin The Wailing Wailers a shekara ta 1966, a shekara ta 1976 Bob Marley ya futar da Rastaman Vibration,wakar da ta samu karbuwa a duniya.
Bob Marley ya rasu ne ranar 11 ga watan Mayu shekarar 1981 a garin Miami na kasar Amurka bayan fama da rashin lafiya.A yau 11 ga watan Mayu,masoyan wakar reggae ko rasta a sassan Duniya na tuni da Bob Marley.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu