Isa ga babban shafi
MDD-Burkina-Guinea-Mali

Sakataren MDD ya bukaci sojojin Burkina, Guinea, Mali su gaggauta mika mulki

Babban magatakaardan majalisar dinkin duniya Antonio Guterres ya yi kira ga gwamnatocin mulkin soji a Burkina Faso, Guinea da Mali da su gaggauta mika mulki ga farar hula.

Antonio Guterres, magatakardar Majalisar Dinkin Duniya.
Antonio Guterres, magatakardar Majalisar Dinkin Duniya. REUTERS - ANDREW KELLY
Talla

Da yake jawabi bayan wata ganawa da shugaban Senegal Macky Sall ranar Lahadi a Dakar, Guterres ya ce sun amince a kan bukatar ci gaba da kira ga gwamnatocin soji a kasashen 3 da gaggauta mika wa fara hula mulki.

Dukkannin kasashen 3 da ke fama da matsalar ta’addanci daga kungiyoyi masu ikirarin jihadi sun fuskanci juyin mulkin soji, inda a Mali, sojoji sun kifar da gwamnatin kasar a watan Agustann 2020 da Mayun 2021, a Guinea, suka hambarar da gwamnatin Kasar a watan Satumban 2021, a yayin da a Burkina Faso, sojoji suka kwace gwamnati a watan Janairun 2022.

Shugaba Macky sall shine shugaban kungiyar ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika, wadda ta dakatar da dukkanin kasashen da sojoji suka karbe gwamnati daga kasancewa mambobinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.