Ministan tsaron Kamaru ya koka kan yawan shingayen binciken ababen hawa
Ministan tsaron kasar Kamaru Joseph Beti Asomo Jeshep ya ja hankalin takaransa na cikin gida Paul Atanga Nji kan yawaitan shingayen binciken ababen hawa da ake samu daga birnin Doula har zuwa Douala zuwa Maroua dake arewacin ciki harda na bogi.
Wallafawa ranar:
Daga cikin shingayen jami’an tsaro 66 da aka lissafa tsakanin birnin Douala (Littoral) zuwa Maroua da dake yankin arewa mai nisa, 27 kachal ne hukuma ta san da su a yayin da ragowar 39 suka kasance ba kan ka'ida ba.
Wannan al’amari dai na kasancewa ga matafiya jerangiyar bata lokaci mai wahalar gaske, kamar yadda ministocin 2 suka sanar a cikin wata sanarwar da suka fitar a ranar 5 ga wannan wata na Afrilu.
Ministan tsaro Joseph Beti Assomo ya ce waddannan shingayen bincike da basa kan ka’ida mahukunta ne suka kafa su. Inda ya bukaci takwaransa na cikin gida Paul Atanga Nji da ya sanar da abukan aikinsa kantomomin kananan hukumomi da na manyan yankuna da gwamnoni da su rage yawan su tare da samar da na gamin gambizar jami’an tsaron.
Sai dai ana ganin mawuyacin abu ne kiran ya samu karbuwa ganin ba a karon farko ke nan ba mahukunta ke kokuwa kan yawaitar shingayen jami’an tsaron kan hanyoyin motar kasar, al’amarin dake haifar da jerangiya ga matafiya ba tare da kwalliya ns biyan kudin sabulu ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu