Isa ga babban shafi
Nijar-ECOWAS

Nijar na karbar bakoncin taron ECOWAS kan ma'adinai da man fetur

A yau laraba ne kungiyar gamayar tattalin arizikin kasshen yankin yammacin Afrika ECOWAS ko CEDEAO tare da hadin guiwar gwamnatin jamhuriyar Nijer za su jagoranci zaman taro na musamman kan abinda ya shafi ma’adinan karkashin kasa da man fetur na tsawon kwanaki 2 a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar

Wasu shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Ecowas / CEDEAO da suka fara taron gaggawa a Ghana saboda juyin mulki a yankin.03/02/2022.
Wasu shugabannin kungiyar kasashen Afirka ta Yamma Ecowas / CEDEAO da suka fara taron gaggawa a Ghana saboda juyin mulki a yankin.03/02/2022. © nigeria vice president office
Talla

Zaman taron mai taken saka kamfanonin hakar ma;adanai da Man fetur wajen ciyar da yankin yammacin Afrika gaba, zai maida hankali ne wajen shirya turbar  da zata samarwa yankin hanyoyi masu armashi karkashin siyasar karabar haraji ga kamfanonin haka ma’adanai dake yankin

Batutun da zaman taron zai kwashe tsawon kwanmaki 3 yana tattaunawa a kai sun hada ne, da batun zuba jari a fannin kamfanonin hakar ma’adanai, duba cancanta, da kuma kula da kare mahalli,

Sanarwar da kungiyar Cedeao ta bayar kan zaman taron ta fayyace   cewa, mahalarta taron za su karkata ne kan maudu’an: da suka shafi batun sarrafa albarkarun da kamfanonin suka haka, da kuma saka kamfanonin hakar ma’adamai wajen daukar matakai da jagoranmci, da kuma nauyin da ya rataya a wuyan kamfanonin wajen samar da ci gaba mai dorewa ga yankunan da suke gudanar da ayukansu a ciki,

Tare da batun binciken albarkatun karkashin kasa a kasashe mambobin kungiyar ta Cedeao.

Zaman taron da zai kwashe tsawon kwanaki uku ana yi a birnin Yami ai hada kwararu, da wakilan gwamnatoci kasashen kungiyar Cedeao.

Kwararu ta fannin hakar ma’adanai da man fetur da kuma shuwagabanin kanana da matsakaitan kamfanoni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.