Gobara ta lakume gidaje da dama a Afrika ta tsakiya
Kusan mutane dubu biyar suka rasa muhallansu a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya bayan gobara ta cinye sansaninsu kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana.
Wallafawa ranar:
Jumullar mutane dubu 4 da 802 ne ke bukatar mazauni cikin gaggawa da kuma abinci da ruwan sha har ma da kayayyakin masarufi a Jamhuriyar Tsakiyar Afrika kamar yadda Anita Cadonau, jami’ar yada labaran ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da jinkai ta sanar.
A ranar Talatar da ta gabata, aka samu ibtila’in gobarar a sansanin Alindao mai tazarar kilomita 500 daga gabashin birnin Bangui.
Mutane 20 ne aka bada rahoton cewa, sun jikkata sakamakon ibtila’in.
Gobarar ta tashi ne bayan wani karamin yaro ya yi kokarin yin girki da man-ja a cewar daya daga cikin wadanda suka shaida lamarin.
Jamhuriyaar Afrika ta Tsakiya dai na cikin kasashen duniya mafi fama da bakin-talauci, yayin da ta fama cikin yakin-basasa a shekara ta 2013 bayan kifar da gwamnatin shugaban kasar na wancan lokacin, Francois Bozize.
Wannan juyin mulkin da ‘yan tawaye suka yi masa, ya haddasa zubar da jini tsakanin dakarun Seleka na Musulmai da kuma Anti-Balaka na Kiristoci.
Faransa da Majalisar Dinkin Duniya ne suka yi uwa-suka-yi makarbiya wajen maido da zaman lafiya a kasar a wancan lokacin, inda har aka gudanar da zaben shugaban kasa. Kodayake har hanzu, ‘yan tawaye na ci gaba da rike da yankuna da dama na kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu