Isa ga babban shafi
Mali-ECOWAS

ECOWAS ta yi watsi da tayin mulkin Sojoji na shekaru 5 a Mali

Mai shiga tsakani na kungiyar kasashen Yammacin Afirka a Mali Goodluch Jonathan, ya ce kungiyar ta Ecowas/Cedeao ba za ta amince da jadawalin da sojoji suka gabatar da cewa sai bayan shekaru biyar ne za a mayar da Mali karkashin cikakken tsari na dimokudiyya ba.

Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da ke matsayin babban mai shiga tsakani na kungiyar ECOWAS a Mali.
Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da ke matsayin babban mai shiga tsakani na kungiyar ECOWAS a Mali. AFP - NIPAH DENNIS
Talla

Goodluck Jonathan, ya yi wannan gargadi ne, lokacin da yake ganawa da shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar ta Mali kanar Assimi Goita jiya laraba a birnin Bamako, gabanin taron da shugabannin kasashen yammacin Afirka za su gudanar a birnin Accra na kasar Ghanaa ranar lahadi mai zuwa kamar dai yadda majiyoyi suka sanar.

Bayan tattaunawar da aka yi ta tsawon sa’o’i biyu tsakanin tsohon shugaban na Najeriya Goodluck Jonathan da kanar Assimi Goita, babu dai wata sanarwa da bangarorin biyu suka fitar da ke yin karin bayani dangane da abubuwan da suka tattauna a kai.

To sai dai a lokacin da yake ganawa da jami’an diflomasiyyar kasashen ketare a birnin Bamako, Jonathan ya ce ‘’Shirin rikon kwaryar shekaru biyar da sojojin suka gabatar, abu ne da ya zarta wa’adin zababben shugaba a kasashe kamar Najeriya’’, saboda haka ba zai samu karbuwa ba.

Gabanin taron shugabannin na Ecowas da za a yi ranar lahadi mai zuwa, tuni ministan harkokin wajen Mali ya ziyarci wasu kasashen yankin da suka hada da Cote d’Ivoire, Burkina Faso, da kuma Saliyo, inda a nan gaba zai je Najeriya da kuma Algeria don gabatar da dalilansu na neman shekaru biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.