Isa ga babban shafi
ECOWAS

Jam'iyyun siyasa sun yi watsi da shirin sojin Mali

Babbar gamayyar jam’iyyun siyasar Mali ta yi watsi da shirin gwamnatin sojin kasar na mika mulki ga farar hula nan da shekaru biyar masu zuwa.

Assimi Goita, shugaban rikon kwaryar mulkin sojin Mali
Assimi Goita, shugaban rikon kwaryar mulkin sojin Mali AFP - ANNIE RISEMBERG
Talla

Tun daga watan Agustan shekarar 2020, sojoji suka mamaye Mali wadda rikici ya daidaita, inda har suka yi juyin mulki sau biyu tare da dage zaben kasar da ya kamata a gudanar cikin watan gobe.

Ministan Harkokin Wajen Mali, Abdoulaye Diop ya gabatar da sabon shirin sojojin ga Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS a ranar Asabar da ta gabata, bayan gudanar da wani taron-gyaran-kasa wanda jam’iyyun siyasar da na ci gaban al’umma suka kaurace masa.

Shirin dai ya kunshi cewa, sai an shafe tsawon shekaru biyar sojojin na gudanar da mulkin rikon kwarya kafin daga bisani su mika ragamar kasar ga farar hula, kuma daga 1 ga wanann wata na Janairu, aka fara lissafin tsawon wa’adin na shekaru biyar.

Gamayyar Jam’iyyun ta ce, wannan sabon tsarin jadawalin ya yi karan-tsaye ga yarjejeniyar mika mulkin, inda kuma ta ce, ya yi hannun riga da muradun ‘yan kasar ta Mali.

A cikin sanarwar da ta fitar, gamayyar ta ce, ta yi watsi da wannan jadawalin wanda ta ce, wani bangare ne kawai ya yi gaban kansa wajen amincewa da shi.

A ranar 9 ga watan nan na Janairu ne, Kungiyar ECOWAS za ta gudanar da wani taro kan batun na Mali a babban birnin Accra na Ghana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.