Isa ga babban shafi
SAUYIN-YANAYI-TSARO

Nijar ta bukaci hada matsalar sauyin yanayi da ayyukan ta'addanci

Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta amince da kudirin hada batun matsalar sauyin yanayi da matsalar tsaron da ake samu a wasu kasashen duniya.

Shugaba Bazoum Mohammed na jagorancin taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya
Shugaba Bazoum Mohammed na jagorancin taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya © Niger Presidency
Talla

Bazoum ya bayyana haka ne lokacin da ya jagoranci taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wanda Nijar ke jagoranci a wannan karo.

Ita dai wannan bukata ta Nijar ta kunshi amincewa da yadda matsalar sauyin yanayi ke tinzira matsalar tsaron dake kaiga kashe kashe a wasu kasashen duniya, musamman yankin Sahel wanda ‘Yan ta’adda suka yiwa kamun kazar kuku.

Shugaban Nijar Bazoum Mohammed da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Anthonio Guterres
Shugaban Nijar Bazoum Mohammed da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Anthonio Guterres © Niger Presidency

Sai dai wannan bukata ta shugaba Bazoum ta gamu da adawa daga kasashen Rasha da China da kuma India, kamar yadda Jakadan Rasha Vassily Nebanza ya sanar.

Nebanza yace a wurin su babu wata alaka tsakanin ayyukan ta’addanci da sauyin yanayi, saboda haka gwamatsa batutuwan guda biyu zai haifar da rudani dangane da wasu kudirorin da Majalisar tayi a baya.

Shugaba Bazoum ya bayyana cewar amincewa da bukatar ta sa zai samar da yanayin da za’a yi aiki tare domin fahimtar illar da sauyin yanayi ke yi wajen iza wutar tashin hankali.

Kasar Faransa ta bayyana goyan bayan ta da kudirin da shugaba Bazoum ya gabatar, inda tace tabbas akwai alaka tsakanin tashe tashen hankulan da ake gani da sauyin yanayi, wanda ke haifar da karancin abinci da rashin ruwan sha.

Ita ma kasar Amurka ta danganta matsalar sauyin yanayin da matsalar tsaro.

A shekarar da ta gabata kasar Jamus ta gabatar da irin wannan kudiri, amma kuma kasar Amurka a karkashin shugaba Donald Trump tayi barazanar hawa kujerar naki idan akayi mahawara akai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.