Isa ga babban shafi
KENYA-TSARO

An kama firsinonin da suka tsere daga gidan yarin Kenya

‘Yan Sanda a kasar Kenya sun yi nasarar kama firsinoni 3 da aka samu da laifin harin ta’addanci wadanda suka tsere daga gidan yarin da ake tsare da su, matakin da ya sa aka kori babban jami’in kula da gidajen yarin kasar baki daya.

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta REUTERS - MONICAH MWANGI
Talla

Hukumomin kasar sun kaddamar da farautar neman mutanen 3 cikin su harda guda da aka yankewa hukuncin shekaru 41 saboda kazamin harin da aka taba gani a Kenya.

Daraktan hukumar kula da binciken laifuffuka ta kasar yace an kama mutanen 3 da suka tsere daga gidan yarin Kamiti ne a wani wuri dake da nisar kilomita 200 daga birnin Nairobi.

Firsinonin da jami'an tsaro suka kama
Firsinonin da jami'an tsaro suka kama © Nation - Kenya

Tuni gwamnatin kasar ta kori shugaban kula da gidajen yarin Wycliffe Ogallo tare da jami’in kula da gidan yarin Kamiti da kuma ma’aikatan gidan yarin guda 7, aka kuma kama su domin gudanar da bincike.

Kafofin yada labaran Kenya sun ce an samu bayanai mabanbanta akan yadda firsinonin 3 suka tsere, yayin da fadar shugaban kasar ta bayyana lamarin a matsayin matsalar tsaro kuma abin kunya.

Daga cikin mutanen 3, an samu Mohammed Ali Abikar da laifin zama ‘dan kungiyar Al Shebaab da kuma taimakawa kungiyar kashe mutane 148 a Jami’ar Garissa a shekarar 2015.

Wasu daga cikin mayakan Al-Shebaab
Wasu daga cikin mayakan Al-Shebaab REUTERS/Feisal Omar

Wannan shine harin ta’addanci mafi muni da Kenya ta gani a tarihin ta, bayan wanda Al Qaeda ta kai a ofishin jakadancin Amurka a shekarar 1998 wanda ya hallaka mutane 213.

Sauran biyun sun hada da Joseph Juma Odhiambo da aka kama a shekarar 2019 lokacin da yake kokarin shiga kungiyar Al Shebaab da Musharaf Abdalla Akhulunga da aka tsare a shekarar 2012 sakamakon yunkurin kai hari majalisar dokokin Kenya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.