Kasar Benin ta karbi kadarorin sarauta kusan 30 da Faransa ta kwace mata
Gwamnatin Benin a ranar Laraba 10 ga watan Nuwamba ta yi maraba da kadarorin sarauta kusan 30 da aka wawashe daga kasar dake yankin Afirka ta yamma a lokacin mulkin mallakar turawan Faransa fiye da shekaru 130 da suka gabata.
Wallafawa ranar:
Shugaban kasar Benin Patrice Talon da ministan al'adu na kasar sun yi tattaki a ranar Talata zuwa birnin Paris domin karbo kayayyakin tarihi guda 26.
Jirgin dake dauke da dukiyar masarautar ya sauka ne da yammacin Laraba a filin jirgin saman Cotonou, inda daruruwan mutane suka taru don nuna girmamawa, da kuma bayyana farin cikinsu.
A karshen watan Oktoba katafaren gidan adana kayan tarihi Quai Branly dake birnin Paris yayi baje-kolin gwamman kayayyakin tarihi da dakarun Faransa suka kwaso daga kasar Benin a zamanin mulkin mallaka, wanda kuma ya zama karo na karshe da za a nuna kayayyakin tarihin a Faransa kafin a mayar da su ga kasar ta Benin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu