Isa ga babban shafi
Rwanda

Amurka da Belgium sun fusata da hukuncin da aka yi wa Rusesabagina

Kasashen Amurka da Belgium sun bayyana cewar ba a yi wa tauraron fim din ‘Hotel Rwanda’, Paul Rusesabagina adalci a shari’ar da aka masa ba, wadda aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 25 a gidan yari.

Paul Rusesabagina
Paul Rusesabagina © AP - Muhizi Olivier
Talla

Sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price ya gabatar bayan yanke hukuncin daurin shekaru 25 da aka yi wa Paul Rusesabagina ta bayyana matukar damuwa dangane da yadda aka gudanar da shari’ar, inda take cewa rahotanni rashin adalcin da ke fitowa daga Rwanda abin dubawa ne.

Ita ma kasar Belgium ta bayyana irin wannan matsayi akan Rusesabagina wanda ta bayyana shi a matsayin dan kasarta, inda ta yi watsi da hukuncin.

Ministar harkokin wajen Belgium, Sophie Wimes ta ce duk da bukatar da kasar ta yi ta gabatar wa hukumomin Rwanda, sun yi watsi da su wajen yanke masa hukunci ba tare da yin adalci ba.

Ita ma 'yar tauraron fina-finan, Carine Kanimba ta ce dama sun san yadda hukuncin zai kaya, kuma alakalan kotun sun bayyana abinda shugaban kama karyar kasar ke bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.