'Yan Mali sun yi zanga-zangar neman karawa sojoji wa'adin mulki
Daruruwan mutane sun yi zanga -zanga a Bamako babban birnin Mali, inda suka bukaci a ba wa shugabannin sojan kasar karin lokaci don tsara zaben da zai sake mayar da mulki ga farar hula.
Wallafawa ranar:
Zanga-zangar ta zo ne bayan da a ranar Alhamis, kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ECOWAS ta ce ba za a sauya jadawalin mika wa farar hula mulki a watan Fabarairu ba.
Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa tsohon shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita a watan Agustan shekarar 2020, sun nada gwamnatin farar hula ta wucin gadi da aka dorawa alhakin mayar da kasar kan mulkin dimokaradiyya.
Sai dai a watan Mayu sojojin a karkashin Kanal Assimi Goita suka sake kwace mulki gami da ayyana shi a matsayin shugaban rikon kwarya.
Goita ya yi alkawarin mutunta wa'adin na shirya zaben na watan Fabrairu, to amma wasu na shakku game da hakan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu