Isa ga babban shafi
Mali-Juyin Mulki

Na rantse da Allah zan kare Mali-Kanar Goita

Jagoran juyin mulkin Mali da aka rantsar a matsayin shugaban kasa na riko Kanar Assimi Goita, ya yi rantsuwa da Allah cewa zai kare kasar, yayin da ya  jaddada aniyarsa ta gudanar da zabe nan da watan Fabairun badi. Tuni shugaban ya nada farar hula a matsayin Firaministansa.

Kanar Assimi Goita
Kanar Assimi Goita REUTERS - FRANCIS KOKOROKO
Talla

Goita wanda ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo karshen gwamnatin zababben shugaban kasa a cikin watan Agustan bara, ya sake kifar da shugaban kasar na riko da Firaministansa a ranar 24 ga watan Mayun bana.

Wannan matakin nasa ya haddasa kurarin diflomasiya tare da tsananta fargabar rikici a kasar wadda  jigo ce a kokarin da ake yi na murkushe mayakan jihadi masu neman mamaye yankin Sahel.

A yayin karbar rantsuwar kama aiki a birnin Bamako, Goita ya rantse da All..da kuma mutanen Mali cewa, zai kare kasar, sannan kuma zai mutunta romon demokuradiya.

Kanar din wanda ya yi ado cikin tufafin sojoji ya kara da cewa, Mali za ta mutunta kudirinta, sannan ya yi alkawarin gudanar da sahihin zaben shugaban kasa a cikin  watan Fabairun shekarar mai zuwa.

Kawo yanzu, babu cikakken bayan kan yadda aminan kasar ta Mali da makotanta za su mayar da martani kan kudirin Goita, lura da cewa, sun caccaki juyin mulkin da ya yi.

Juyin mulkin ne ya sanya Kungiyar ECOWAS ta dakatar da Mali daga cikinta, sannan ta yi kira da a nada Firaminista farar hula a kasar ta yammacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.