Sojojin Guinea sun hana Alpha Conde gudun hijira
Shugabannin sojan Guinea sun ce ba za su bari hambararren shugaban kasar Alpha Conde ya yi gudun hijira ba, bayan da masu shiga tsakani kungiyar ECOWAS suka yi kokarin matsa lamba don ganin an sake shi.
Wallafawa ranar:
Sanarwar gwamnatin sojin ta Guinea a ranar Juma'a ta zo ne bayan kungiyar yankin yammacin Afirka da aka fi sani da ECOWAS ta gana da shugaban ta Kanal Mamady Doumbouya da ya jagoranci juyin mulkin da a farkon wannan wata na Satumba.
Bayan ganawa da Kanal Dambouya, jagoran kungiyar ECOWAS, kuma shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, da shugaban Ivory Coast, Alassane Ouattara, sun ziyarci Conde, wanda aka tsare tun lokacin da aka hambarar da shi a ranar 5 ga watan Satumba bayan fiye da shekaru 10 a kan mulki.
A ranar Alhamis, shugabannin kasashen Afrika ta yamma suka kakaba wa jagororin juyin mulkin Guinea takunkumi, kana suka bukaci a gudanar da zabe nan da watanni 6 don maido da mulkin demokaradiyya cikin hanzari a kasar, bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Alpha Conde a farkon wannan wata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu