Isa ga babban shafi
Kamaru - Afirka ta tsakiya

Kamaru ta tsare wasu 'yan tawayen Afirka ta Tsakiya a cikin kasar ta

Jami’an tsaron Kamaru sun tsare wasu mambobin wata kungiyar tawayen Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da suka shigo Ngaudere dake jihar Adamawan kasar, inda suke kokarin aikata ayyukan garkuwa da mutane.

Tsoffin 'yan tawayen Seleka a Afirka ta Tsakiya dauke da makamai a birnin Bangui. 5/12/2013.
Tsoffin 'yan tawayen Seleka a Afirka ta Tsakiya dauke da makamai a birnin Bangui. 5/12/2013. AFP/Sia Kambou
Talla

Rahotanni daga Ngaunderen kasar ta Kamaru dake iyaka da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar Afirkan na cewa, Jami’an jandarmomi ne sukayi nasarar cafke wasu mayakan tawayen kungiyar tawayen 3K, bayan da suka samu bayanan sirri.

Kwamandan rundunar Jandarmomin na jihar Adamawa, Kanal Jean Pierre Kagombe Keffiene yayin zantawa da manema labarai dangane da kamen, yace bayan nasarar cafke mahara biyu, suka samu damar kame wasu karin maharan da masu taimaka musu guda 4.

A cewar jami’in mayakan ‘yan tawayen da suka shigo kasar ta Kamaru ta hanyar amfani da wasu takardun bogi, sun kasance cikin kungoyin ‘yan tawayen da suka hana gwamnatin shugaba Faustin Arkange Touadera a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sakat tun a shekarar 2015, tare da haddasa yakin basasar da yayi sanadiyar mutuwar dubban mutane.

Mayakan kungiyoyin ‘yan tawaye na kutsawa kasar Kamaru a kai-akai, inda suke garkuwa da mutane masamman jami’an gwamnati, don karban kudin fansa ko gabatar da wasu bukatu na daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.