Isa ga babban shafi
Kamaru-MDD

Sojojin Kamaru suna yajin aiki saboda kin biyansu alawus

A kasar Kamaru, sojoji sama da dari biyu ne suka gudanar da zanga-zanga jiya laraba a birnin Yaounde, inda suke neman a biya su kudadensu na alawus, bayan sun yi aikin wanzar da zaman lafiya a makociyar kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Dakarun wanzan da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya
Dakarun wanzan da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya AFP PHOTO/PACOME PABANDJI
Talla

Sojojin wadanda ke sanye da kayan sojan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, sun yi tattaki na tsawon kilomita hudu daga barikinsu na Ekounou zuwa babbar cibiyar sojan kasar da ke birnin Yaounde, to sai dai bayan hana su shiga a barikin sun wuce zuwa Majalisar dokokin kasar, domin gabatar da kukansu ga ‘yan majalisar.

Majiyoyi sun ce yanzu haka akwai sojojin kasar dubu daya da dari uku da ke jiran a biya su kudadensu na alawus bayan kammala aikin wanzar da zaman lafiya karkashin inuwar Majalisar ta Dinkin Duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.