An daure sojojin Gabon da suka yi yunkurin juyin mulki a 2019
An yanke wa sojojin Gabon uku hukuncin daurin shekaru 15 a kidan kaso, sakamakon rawar da suka taka a juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekarar 2019.
Wallafawa ranar:
Babban Mai gabatar da karar gwamnatin Gabon wanda ya sanar da hukuncin a wannan Alhamis, yace cikin sojojin ukun, har da Laftanar Kelly Ondo Obiang wanda ke cikin rundunar tsaron fadar shugaban kasa, da ya bayyana a kafar a talabijin din kasar ranar 7 ga watan Janairun shekarar 2019, inda ya yi kira ga jama’a da su fito suyi bore nuna goyan baya ga yunkurin na juyin Mulki.
An wanke mutane shida
Acewar bababn mai gabatar da karar, kotun ta kuma wanke wasu mutane shida da ake tuhuma kan yankurin na hambarar da shugaban kasa Ali Bongo Odimba da baiyi nasaraba, cikinsu harda 'yan sanda biyar da farar hula guda.
Ana ganin hukuncin nada sassauci, domin kuwa tuhuma ne da ya shafi yiwa tsaron kasa zagon kasa, wanda yakan kai ga hukuncin daurin rai-da-rai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu