Isa ga babban shafi
Gabon

Bongo zai koma Gabon bayan yunkurin yi masa juyin mulki

Ana sa ran shugaban Gabon, Ali Bongo ya koma gida a ranar Talata bayan shafe sama da watanni biyu yana jinya a kasar waje, abin da ake kallo a matsayin musabbabin yunkurin wasu sojin kasar na yi masa juyin mulkin da bai yi nasara ba.

Shugaban Gabon Ali Bongo Ondimba
Shugaban Gabon Ali Bongo Ondimba REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Mr. Bongo mai shekaru 59 ya gamu da rashin lafiya ne a daidai lokacin da yake halartar wani taron tattalin arziki a Saudiya a cikin watan Oktoban da ya gabata, yayin da aka garzaya da shi kasar Morocco domin kula da lafiyarsa.

An yi ta yada rade-radin cewa, shugaban ya rasu kafin daga bisani mataimakinsa ya shaida wa al’ummar kasar cewa, yana raye amma ya na fama da cutar shanyewar barin jiki.

Shugaban ya yi wa al’ummar kasar jawabin shiga sabuwar shekara a wani faifai da aka nada a Morocco, kana aka watsa ta kafar talabijin din kasar.

Sai dai jawabin nasa ya gamu da suka musamman daga bangaren ‘yan adawa da ke cewa, shugaban bai yi jawabi mai tsawo ba kamar yadda aka saba, kuma babu shakka yana cikin mawuyacin hali a cewarsu.

A makon jiya ne, aka yi nasarar kawar da yunkurin wasu tsirarun sojoji na yi masa juyin mulki, in da jami’an tsaro suka kama shugaban masu juyin mulkin tare da kashe mutun biyu daga cikin mukarrabansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.