Isa ga babban shafi
Masar

An kama tsohon dan Majalisar Masar da laifin fataucin kayayyakin tarihi 201

‘Yan sandan Masar sun kame wani tsohon dan majalisar kasar bisa tuhumarsa da laifin fasakaurin kayayyakin tarihin da suka hada da na dadaddiyar masarautar Fir’auna, daular Rum da kuma ta Girka zuwa kasashen ketare.

Wasu gumakan tarihi masarautar Fir'auna a birnin Cairo na kasar Masar.
Wasu gumakan tarihi masarautar Fir'auna a birnin Cairo na kasar Masar. AFP/File
Talla

Adadin kayayyakin tarihin 201 ake zardin tsohon dan majalisar da sacewa, wanda a baya ya taba fuskantar tuhume-tuhume kan tonon kasa da zummar gano ababen tarihi a sassan Masar ba tare da izinin hukuma ba.

A karkashin dokokin Masar, duk wanda aka samu da laifin fasakaurin kayayyakin tarihi zai fuskanci hukuncin daurin rai da rai ne, da kuma biyan tara mai tsanani.

A baya bayan nan, wani lauyan gwamnatin Masar ya sanar da karbo wasu kayayyakin tarihi akalla 115 da aka sace daga Paris, bayan da suka shafe shekaru biyu suna kokarin gano su tare da hadin gwiwar hukumomin Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.