Isa ga babban shafi
Masar-Suez

Masar ta cimma jituwa da jirgin Ever Given kan diyyar mashigin Suez

Masar da masu jirgin dakon kaya na Ever Given sun cimma jituwa kan diyyar da mahukuntan kasar suka bukaci biya gabanin sakin jirgin wanda ya tokare mashigin ruwan Suez tare da haddasa gagarumar asara a cikin watan Maris na shekarar nan.

Jirgin Ever Given da ya makale a mashigin ruwan Suez ranar 23 ga watan Maris din shekarar nan.
Jirgin Ever Given da ya makale a mashigin ruwan Suez ranar 23 ga watan Maris din shekarar nan. - Satellite image ©2021 Maxar Technologies/AFP
Talla

Tsawon lokaci aka dauka hukumar da ke kula da mashigin ruwan ta Suez da mamallakan jirgin game da makalewar da ya yi na tsawon kwanaki 6 wanda ya haddasawa Masar asarar makudan kudaden shigar da ta ke samu daga mashigin.

A karon farko, mahukuntan Masar sun bukaci kamfanin da ke da jirgin ya biyasu diyyar dala miliyan 900 don rage radadin kudin shigar da ya yiwa kasar asarar samu, yayinda bayan jerangiyar tattaunawa suka sassauto da farashin zuwa dala miliyan 550.

Sai dai bayan doguwar ganawar bangarorin biyu a jiya laraba, dukkaninsu sun sanar da cimma jituwa yayinda suka ce suna gab da rattaba hannu kan yarjejeniya, ko da ya ke babu karini bayan kan yawan kudin da kamfanin na Ever Given mai kula da jirgin na Japan zai biya.

Tun bayan nasarar janye jirgin daga makalewar da ya yi laka yayin wuce ta mashigin ruwan na Suez mallakin Masar ne, kasar ke ci gaba da tsare da shi saboda asarar da ya haddasa mata a tsawon kwanakin da ya yi ba tare da barin wasu jirage sun wuce ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.