Isa ga babban shafi
Masar-Suez

Masar ta kwace jirgin ruwan Japan da ya makale mashigin ruwan Suez

Hukumomin Kasar Masar sun kwace katafaren jirgin ruwan nan wanda karkacewar sa ta yi sanadiyyar rufe hanyar Suez wanda ya hana jiragen ruwa sama da 400 wucewa na kwanaki a yankin.

Katafaren jirgin MV Ever Given mallakin Japan da ya makale a mashigin ruwan Suez na Masar.
Katafaren jirgin MV Ever Given mallakin Japan da ya makale a mashigin ruwan Suez na Masar. - Satellite image ©2021 Maxar Technologies/AFP
Talla

Wata kotu a Masar ta bada umurnin kama jirgin ruwan mai dauke da nauyin tan dubu 200 har sai ya biya diyyar Dala miliyan 900 da gwamnatin kasar Masar ta bukata saboda matsalar da ya haifar na kwanaki 6.

Hukumomin sufuri sun ce jirgin wanda fadin sa ya kai filayen kwallon kafa guda 4 ya yi sanadiyar hana dukiyar da ta kai sama da dala biliyan 9 da rabi wucewa tsakanin Asia da Turai lokacin da aka samu matsalar.

Masar ta yi asarar da ta kai tsakanin Dala miliyan 12 zuwa miliyan 15 na harajin da ta ke samu kowacce rana saboda jiragen da su ke wucewa ta hanyar kowacce rana.

Jirgin mallakar kasar Japan amma kuma dauke da tutar Panama da ke karkashin kulawar Taiwan ya yi sanadiyar hana jiragen ruwa 420 wucewa lokacin da ya makale a tsakanin mashigin ruwan Suez daga ranar 23 ga watan Maris zuwa ranar 29 ga wata.

A karkashin dokokin Masar hukumomin kasar na iya rike jirgin har zuwa lokacin da za’a biya ta diyyar da ta bukata kafin sakin shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.