Isa ga babban shafi
Habasha-Zabe

Ana dakon sakamakon zaben 'yan majalisar dokoki a Habasha

Al’ummar Habasha sun kada kuri’a a zaben da aka yi ittifakin cewa shine mafi tsafta a dimokaradiyance, a kasar, sai dai kuma an yi zaben ne a daidai lokacin da yankin Tigaray da yaki ya daidaita ke fama da matsanancin yunwa.

firaministan Habasha Abiy Ahmed yayin da yake kada kuria'a a zaben 'yan majalisar dokokin kasar.
firaministan Habasha Abiy Ahmed yayin da yake kada kuria'a a zaben 'yan majalisar dokokin kasar. REUTERS - TIKSA NEGERI
Talla

Wannan ne zabe na farko a karkashin jagorancin Firamitsan kasar Abiy Ahmed, kasar da ita ce ta 2 a yawan jama’a a nahiyar Afrika tun da  ya dare karagar mulki a shekaru 3 da suka wuce.

Jigo a cikin sauye sauyen da Firaministan, wanda ya lashe kyautar zaman lafiya ta Nobel ya kawo shine sakar wa kowa mara ya taka rawa a siyasar kasar kana ya yi afuwa ga fursunoni tare da tarbar masu laifin da suka dawo kasar.

Da karfe shida agogon GMT aka rufe rumfunan zabe, bayan da aka tsawaita kada kuri’a  da sa’o’i 3 da bai wa duk wanda ya halarci rumfar zabe kada kuri’a.

Babbar matsalar da ke tattare da wannan zabe dai ita ce rashin kada kuri’a a kashi 1 cikin 5 na mazabun kasar 547, musamman a yankunan da ke da matukar hadari sakamakon rashin zaman lafiya.

Jam’iyyar Firaminista Abiy Ahmed ne dai ta tsaida ‘yan takara mafi yawa a zaben, kuma ake sa ran za ta lashe mafi rinjayen kujeru a majalisar dokokin kasar.

Yanzu ana nan ana dakon sakamakon zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.