Isa ga babban shafi
ECOWAS - Mali

ECOWAS na taro kan juyin mulkin sojoji a Mali

Shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ke taro a Accra babban birnin kasar Ghana, domin tattaunawa kan yadda za su warware rikicin siyasar kasar, da sojoji suka yi juyin mulki sau 2 cikin watanni 9.

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo kuma shugaban kungiyar ECOWAS, yayin jagorantar taron kungiyar a birnin Accra.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo kuma shugaban kungiyar ECOWAS, yayin jagorantar taron kungiyar a birnin Accra. © Reuters
Talla

Daga cikin shugabannin dake halartar taron na yau dai akwai shugaban sojojin da suka yi juyin mulkin na Mali Kanal Assimi Goita, shugaban Ivory Coast alassane Ouattara, shugaban Najeriya Muhd Buhari da kuma Christian Marc Kabore na Burkina Faso.

Kafin taron na yau Lahadi dai, kungiyar at ECOWAS tayi barazanar kakabawa gwamnatin sojojin ta Mali takunkumi, bisa abinda ta kira jefa makomar kasar cikin hatsari da suka yi.

Kanal Assimi Goïta, da ya jagoranci juyin mulki sau biyu a Mali cikin watanni 9.
Kanal Assimi Goïta, da ya jagoranci juyin mulki sau biyu a Mali cikin watanni 9. AP

A ranar litinin da ta gabata, Kanal Assimi Goita da ya jagoranci yiwa tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Kieta juyin Mulki, ya sake kwace mulkin bayan tsare shugaban rikon kwarya na farar hula Bah Ndaw da Firaministansa Moctar Ouane wadanda aka saki a ranar Alhamis bayan da suka yi Murabus.

Kanal Goita ya jagoranci juyin mulkin farko ne a watan Agustan 2020 bayan da tsohon shugaba Keita ya fuskanci zanga-zangar gama gari ta neman yayi murabus saboda gazawarsa wajen magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.