ECOWAS za ta yi taron gaggawa kan rikicin siyasar Mali
Shugabannin kasashen dake kungiyar ECOWAS za su gudanar da wani taron gaggawa ranar lahadi mai zuwa domin tattauna rikicin siyasar kasar Mali sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wajen kawar da gwamnatin rikon kwaryar kasar.
Wallafawa ranar:
Kungiyar tayi barazanar sake sanyawa kasar Mali takunkumi sakamakon juyin mulkin wanda ya kawo karshe shirin mika mulki ga fararen hula a shekara mai zuwa.
Shugaban rikon kwaryar kasar Bah Ndaw da Firaministan sa Moctar Ouane sun aje mukaman su bayan tsare su da sojoji suka yi, yayin da shugaban sojin Assimi Goita ya bayyana kan sa a matsayin jagoran sabuwar gwamnatin sojin.
Tawagar kungiyar ECOWAS a karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ta ziyarci Mali inda ta gana da sojojin da kuma shugabannin da aka tube.
Tuni Jonathan ya koma Najeriya inda ya gabatar da rahotan ziyarar sa ga shugaba Muhammadu Buhari kafin taron da zai gudana a karshen wannan mako.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu