Isa ga babban shafi
Najeriya-Nijar

Jamhuriyyar Nijar ta sanar da ganin jinjirin watan Shawwal

Jamhuriyyar Nijar ta sanar da ganin jinjirin watan Shawwal yau Talata, wanda ke nuna kasar za ta yi Sallar Idi a gobe Laraba, sanarwar da ke zuwa dai dai lokacin da Najeriya ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar na ta Idin saboda gaza ganin jinjirin watan a sassanta.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Jamhuriyyar Nijar da Najeriyar makwabtan juna ke salla a mabanbantan ranaku ba.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Jamhuriyyar Nijar da Najeriyar makwabtan juna ke salla a mabanbantan ranaku ba. Sajjad HUSSAIN AFP
Talla

Firaministan Nijar Ouhoumoudou Mahamadou, ne ya sanar da ganin jinjirin watan a sassan kasar kusan 10, ciki har da yankunan da ke makwabtaka da Najeriya wadda har zuwa yanzu ba ta kai ga ganin jinjirin watan ba.

Mai Alfarma sarkin Musulmin Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar na III bayan kammala ganawa da kwamiti na musamman kan ganin watan na Shawwal ya ce kwamitin bai samu rahoton ganin jinjirin watan ba.

Cikin Sanarwar da fadar mai alfarma sarkin Musulmin ta fitar ta ce sai a ranar Alhamis 13 ga watan Mayu ne kasar za ta gudanar da sallar Idi don kawo karshen azumin watan Ramadana.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Jamhuriyyar Nijar da Najeriyar makwabtan juna ke sallah a mabanbantan ranaku ba.

Ko a bara ma Najeriya ta yi azumin Ramadana 30, wanda ya haddasa rarrabuwar kai ta yadda wasu suka gudanar da Sallar Idinsu daban. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.