Rikicin kabilanci ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 100 a Chadi
A kasar Chadi, Kimanin mutane 100 aka kashe a wani rikicin kabilanci a Mouraye Salamat dake kudu maso gabashin ƙasar.
Wallafawa ranar:
Rikici da Hukumar Kare Hakkin Dan-Adam ta kasa, ta zargi gwamnatin da nuna halin ko-in-kula tare da yin kira da a dauki kwararan matakai don fuskantar abin da ta kira laifukan cin zarafin bil'adama.
Rahotanni suka ce, an dauki tsawon kwanaki, wasu kabilun manoma da makiyaya a kauyukan yankin Mouraye na farmakan juna da kibiyoyi da bindigogi.
Zuwa wayewar safiyar Asabar, yawan mutanen da suka mutu ya haura dari kuma Shugaban Hukumar Kare Hakkin Dan-Adam ta Kasa, Djidda Oumar, ya daura laifin ga gwamnati.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu