Isa ga babban shafi
Chadi

Fararen hula a Chadi na shirin jerin gwanon adawa da gwamnati

Kungiyoyin Fararen hula a Chadi sun sha alwashin gudanar da jerin gwanon adawa da gwamnatin kasar saboda matakan da ta ke dauka wanda ke haifar da tsadar rayuwa duk da haramta zanga-zangar da aka yi.

Shugaban kasar Chadi Idriss Déby
Shugaban kasar Chadi Idriss Déby Ludovic MARIN / AFP
Talla

Mahamat Nour Ibedou, shugaban kawancen kungiyoyin fararen hular kasar ya ce sun gudanar da taron inda suka nuna rahsin amincewar su da haramta zanga-zangar lumana da aka yi a kasar.

A watan jiya, magoya bayan gwamnati sun gudanar da zanga-zangar nuna bacin ran su da haramtawa 'yan kasar zuwa Amurka, amma kuma yanzu da ake shirin zanga-zangar adawa da manufofin gwamnati sai hukumomi na cewa an hana zanga-zangar a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.