Isa ga babban shafi
Najeriya-Chadi

Idriss Deby ya ziyarci Buhari a Abuja

Shugaban kasar Chadi Idris Deby Itno ya ziyarci Najeriya inda ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari kan batutuwan da suka shafi kasashen biyu.

Shugaban Chadi Idriss Deby Itno
Shugaban Chadi Idriss Deby Itno BRAHIM ADJI / AFP
Talla

Fadar shugaban Najeriya ba ta yi bayani kan abubuwan da shugabannin suka tattauna a Abuja ba, amma ziyarar Deby na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya da Nijar da Chadi da kuma Kamaru ke fuskantar karuwar hare-haren mayakan Boko Haram.

A makwanni biyu da suka gabata, hare-haren ta’addanci sun yi sanadiyar hallaka mutane sama da 200 a Jamhuriyar Nijar.

Shugaba Idris Deby da ya kwashe shekaru sama da 30 a karagar mulki yana  takara a zaben da za’ayi ranar 11 ga watan gobe.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.