Isa ga babban shafi
Chadi

Idriss Deby ya samu damar sake neman tazarce kan mulkin Chadi

Jam’iyyar dake mulkin kasar Chadi ta amince da takarar shugaba Idriss Deby domin neman wa’adi na 6 a zaben da za’ayi a wannan shekara.

Idriss Déby, shugaban kasar Chadi.
Idriss Déby, shugaban kasar Chadi. Ludovic Marin/AP Photo
Talla

Shugaba Deby wanda ke cigaba da samun goyan bayan kasashen duniya duk da salon mulkinsa na kama karya ya yabawa magoya Jam’iyyar sa ta ‘Patriotic Salvation Front’ da suka goya masa baya.

Deby yace ya dauki dogon lokaci yana nazari kafin amincewa da bukatar magoya bayan sa na sake tsayawa takara.

Sai dai jam’iyyun adawar kasar sun bukaci jama’ar kasar da su gudanar da zanga zanga yau asabar, amma hukumomin kasar sun haramta musu saboda dalilan tsaro.

A ranar talatar da ta gabata, jam’iyyun adawa 12 suka bayyana aniyar su ta aiki tare da kuma gabatar da dan takara guda domin karawa da Deby a zaben da za’ayi ranar 11 ga watan Afrilu.

Shugaba Idris Deby ya karbi ragamar mulkin Chadi a watan Disambar shekarar 1990 lokacin da ya kifar da gwamnatin shugaba Hissene Habre, kuma tun daga lokacin ake zaben shi a matsayin shugaban kasa, abinda ya bashi damar samun nasara har sau 5, sakamakon sauya kundin tsarin mulkin da akayi a shekarar 2005 wanda ya cire wa’adin shugabancin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.