Isa ga babban shafi
Chadi-Zabe

'Yan takarar Jam'iyyun adawar Chadi 3 sun janye daga zaben shugaban kasa

‘Yan takara uku daga jam’iyyun adawar Chadi sun janye daga jerin mutum 8 da ke shirin fafatawa da shugaba Idris Deby a zaben kasar na ranar 11 ga watan gobe, janyewar da ke biyo bayan zarge zargen dirar mikiya da jami’an tsaron kasar sukayi wa ‘yan adawa a baya-bayan nan.

Shugaban kasar Chadi Idriss Déby da ke neman wa'adi na 6 a zaben kasar da ke tafe a watan gobe.
Shugaban kasar Chadi Idriss Déby da ke neman wa'adi na 6 a zaben kasar da ke tafe a watan gobe. Ludovic Marin /Pool via REUTERS
Talla

Janyewar ‘yan takarar 3 ya rage adadin masu tsayawa takara zuwa mutum 6 cikinsu har da shugaban kasar ta chadi Idris Deby Itno, wanda ya shafe tsawon shekaru 30 yana mulkar kasar yayinda ya ke sake neman tazarce a wa’adi na 6.

Theophile Bongoro Bebzoune wanda sabon shiga ne karkashin gamayyar jam’iyyun ‘yan adawa ta Victory Alliance ne ya shelantawa kamfanin dillancin labaran Faransa matakin ko da ya ke baiyi karin bayan ikan dalilan janyewar ba.

Kazalika Mahamat Yosko Brahim, da kuma Ngarlejy Yorongar da ya kasance tsohon na hannun damar Deby sun shaida janyewarsu daga takarar zaben, inda Brahim ya bayyana cewar yanayin da ake ciki yanzu haka ba zai bada damar gudanar da sahihin zabe ba yayinda Yorongar ke cewa jam’iyyun adawa na fafutuka da rashin adalci ga al’ummar kasa, ga kuma matsalar tsaro.

Sanarwar ta su na zuwa ne kwana guda bayan da Kotun Kolin kasar ta Chadi ta amince da takarar mutane 8 a zaben da ake shirin gudanarwa, yayin da ta yi watsi da takarar wasu guda 7.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.