Isa ga babban shafi
Nijar

Shirye shirye sun kankama kan zaben Jamhuriyar Nijar zagaye na 2

Hukumomin Jamhuriyar Nijar na cigaba da shirye-shiryen gudanar da zaben shugabancin kasar zagaye na biyu cikin nasara.

Bazoum Mohammed da abokin takarar sa Mahamane Ousmane
Bazoum Mohammed da abokin takarar sa Mahamane Ousmane RFI Hausa
Talla

Sabanin ‘yan takara 28 da suka kara a zagayen farko, a yanzu ‘yan takara 2 ne za su fafata a zaben shugabancin na Nijar zagaye na 2, da suka hada da Mahaman Usman na jam’iyyar RDR Canji da kuma Bazum Muhammad na jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya.

Yayin jagorantar yakin neman zabensa Mahaman Usman na RDR ya yi ikirarin cewa shi ne zai lashe zaben zagaye na biyu da zai wakana a ranar Lahadi mai zuwa, tare da bayyana dalilansa.

01:01

Mahaman Usman dan takarar shugabancin Jamhuriyar Nijar na jam’iyyar RDR Canji

Salisu Isah

Sai dai dan takarar jam’iya mai mulki ta PNDS Tarayya Bazum Mohamed da shi me ke da kwarin gwiwar samun nasara, ya bayyana daukar wasu matakan gaggawa idan ya lashe zaben da zai gudana a ranar Lahadi mai zuwa, matakan da yace sune a gaba, sun hada da sha’anin tsaro da kuma ilimi, yayin taron gangamin da ya jagoranta a garin Maradi.

01:02

Bazum Muhammad dan takarar shugabancin Jamhuriyar Nijar na jam’iyya mai mulki ta PNDS Tarayya

Salisu Isah

A zagayen farko na zaben da ya gudana dai, kashi 39 na kuri’un da aka kada Bazum Muhammad ya samu, yayin da Mahaman Usman ya samu kashi 17.

Zaben na Nijar na zuwa ne yayinda dakarun kasar ke cigaba da kokarin murkushe hare-haren ‘yan ta’adda akan iyakarta da Najeriya daga barin kudu maso gabashi, sai kuma iyakar ta da Mali dake yankin kudu maso yammacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.