Isa ga babban shafi
Najeriya

Tsohon gwamnan Legas, Lateef Jakande, ya rasu yana da shekaru 91

Rohotanni daga jihar Legas na cewa yau Alhamis tsohon gwamnan jihar, Alhaji Lateef Jakande ya rasu yana da shekaru 91 a duniya.

Tsohon gwamnan jihar Legas Alhaji Lateef Jakande da takwaransa mai ci Babajide Sanwo-Olu
Tsohon gwamnan jihar Legas Alhaji Lateef Jakande da takwaransa mai ci Babajide Sanwo-Olu Sanwo-Olu
Talla

Gwamnan jihar Legas mai ci yanzu, Babajide Sanwo-Olu, ya tabbatar da rasuwar dattijon cikin wata sanarwa da ya fitar yau Alhamis.

Babajide wanda ya fitar da sanarwar ta shafukansa na sada zumuntar intanet, ya fara da bayyana cewar “daga Allah muka fito kuma gareshi za mu koma” kafin ya jinjinawa marigayin kan namijin kokarin da yayi tsawon rayuwansa yana bautawa jihar Legas.

Sanwo – Olu yace, jihar ta yi babban rashi, kuma zasu ci gaba da tunawa da shi tare da kwai-kwayon ayyukansa na alheri da cigaban kasa.

Gwamna Babajide yace “A madadin Gwamnati da jama’ar Jihar Legas, ina son in bayyana ta’aziyya ga iyalai, ‘yan uwan ​​Baba Jakande da abokan arziki”

"Allah Ya ba shi Aljanat Firdaus, Aamin."

Alhaji Lateef Jakande, wanda aka fi sani da Baba Kekere, shine Gwamnan farar hula na farko a jihar Legas da ya jagoranci jihar tskanin ranar 1 ga watan Oktoban shekarar 1979 zuwa 31 ga watan Disambar 1983, kuma ya kawo ci gaba mai yawa ga jihar, karkashin kudurori biyar na Jam’iyyar Unity Party of Nigeria (UPN) da tsohon Firimiyan Yamma, Cif Obafemi Awolowo ya kafa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.