Isa ga babban shafi
Wasanni

Morocco ta kare kambinta na gasar CHAN

Kasar Morocco ta ci gaba da rike kambin ta na gasar kwallon kafar Afirka `yan wasan cikin gida, wato CHAN, bayan doke Mali da ci 2-0 a wasan da aka karkare ranar Lahadi, a Yaounde babban birnin kasar Kamaru.

Wasu 'yan wasan kasar Morocco yayin murnar lashe gasar CHAN
Wasu 'yan wasan kasar Morocco yayin murnar lashe gasar CHAN CAF
Talla

Kasar Morocco, wacce ta lashe gasar ta shekarar 2018 da ta karbi bakwanci, ta kafa tarihin zama kasar farko da ta ci gaba da rike kambin Gasar ta Kasashen Afirka da aka kebewa `yan wasan dake taka leda a cikin gida.

Dan wasan gaba na Marocco Soufiane Bouftini ne ya fara jefawa kungiyar kwallo a mintuna na 69 da soma wasa kafin daga bisani kyaftin din tawagar Ayoub el Kaabi ya kara ta biyu bayan minti 10 da kwallon farko, matakin da ya baiwa `kungiyar dake arewacin Afirka damar kafa tarihin lashe gasar sau biyu a jere.

Amma fa sun ji jiki a hannun Mali dake neman wannan kofi ruwa a jallo, bayan da suka taba kawar da wannan dama a shekarar 2016.

Wasanni biyar Morocco ta ci cikin shida da ta buga a kuma taci kwallaye 15 a gasar da kasar Kamaru ta karbi bakwanci.

To sai dai Kamaru mai masaukin baki ta gaza zuwa wasan karshe, ta tsaya a mataki na 4, bayan da Guinea ta doke ta da ci 2-0 a wasan neman mataki na uku da aka kara a Doula ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.