Isa ga babban shafi
Wasanni

Morocco ta lallasa Kamaru da 4-0 duk da kulunboton wasu magoya baya

Kasar Kamaru ta gaza kaiwa zagayen karshe na gasar cin kofin kasashen Afrika ta ‘yan wasan da suke murza tamaula a cikin gida ta CHAN.

Dan wasan Morocco yayin murnar lallasa Kamaru a gasar cin kofin kasashen Afrika ta CHAN.
Dan wasan Morocco yayin murnar lallasa Kamaru a gasar cin kofin kasashen Afrika ta CHAN. CAFOnline.com
Talla

A ranar Laraba ne dai aka buga wasannin kusa da na karshe a gasar ta CHAN, inda Morocco ta lallasa Kamaru da kwallaye 4-0, yayin da kuma Mali ta doke Guinea da kwallaye 5-4 na bugun daga kai sai mai tsaron raga wato fanareti, bayan da suka tashi canjaras babu ci, a tsawon mintuna 90 da dan karin lokaci da suka fafata.

Wasan na Kamaru da Morroco dai ya dauki hankula la’akari da yadda mai masaukin bakin taji jiki, duk da cewar wasu hotunan bidiyo da suka yi ta yawo a kafafen sadarwa sun nuna yadda wasu magoya bayan tawagar kwallon ta Kamaru suka rika kulunboto iri-iri don ganin ta samu nasara ciki har da cinye zakara danye, da kuma wasu nau’ikan tsatsube-tsatsube.

A halin yanzu za a fafata wasan neman gurbi na uku tsakanin Kamaru da ke karbar bakuncin gasar ta CHAN da Guinea a ranar 6 ga watan Fabarairu. Yayin da kuma za a fafata wasan karshe a ranar 7 ga watan na Fabarairu tsakanin Mali da Morocco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.