Isa ga babban shafi
Afrika

Shugaban Kungiyar Tarayar Afrika Moussa Faki Ya Sami Zarcewa Wa'adi Na Biyu

Tsohon Firaministan Chadi Moussa Faki Mahamat ya sami zarcewa wa'adi na biyu na tsawon shekaru hudu na shugabancin kungiyar Tarayar Afrika.

Moussa Faki Mahamat Shugaban Kungiyar Tarayar Afrika
Moussa Faki Mahamat Shugaban Kungiyar Tarayar Afrika RFI
Talla

Shugabannin kasashen kungiyar suka amince da wannan zarcewa a taron su ta bidiyo na kwanaki biyu da suka fara Asabar.

Faki wanda ya kasance babu hamayya a takaran ta sa ya sami kuri'u 51 daga cikin wakilai 55 a zaben da aka yi cikin sirri.

Taron na shugabannin kasashen Africa ta bidiyo na zuwa ne shekara daya bayan da kasar Masar ta sami mutun na farko da ya harbu da kwayar cutar Coronavirus, al’amarinda ya haifar da fargaba a kasashen nahiyar.

Taron na kwanaki biyu ta bidiyo na duba matsalar cutar Coronavirus a nahiyar da sauran matsalolin rashin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.