Isa ga babban shafi
Afrika

Bazoum zai kara da Ousmane a zaben Nijar

A Jamhuriyar Nijar,kotun fasalta kudin tsarin mulkin kasar ta fitar da sakamakon zaben farko na watan Disemba shekarar da ta shude, inda ta bayyana cewa yan takara Bazoum Mohammed daga jam’iyya mai mulki PNDS da Mahamane Ousmane daga jam’iyyar RDR Canji.

Bazoum Mohammed da abokin takarar sa Mahamane Ousmane
Bazoum Mohammed da abokin takarar sa Mahamane Ousmane RFI Hausa
Talla

Kotun fasalta kudin tsarin mulkin kasar ta Nijar ta yi watsi da akasarin karar da jam’iyyun siyasar kasar suka shiga na cewa an tafka magudi yayin zaben shugaban kasa zagayen farko.

A cewar jami’an kotun dan takara Bazoum Mohamed daga PNDS ya samu kashi 39,67% na kuri’u da aka kada,yayinda Mahamane Ousmane ya tashi da kusan kashi 16,99% kuri’u da aka kada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.