Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Farfesa Kamilu Sani Fagge kan fargabar sake kazancewar rikicin Libya

Wallafawa ranar:

A halin yanzu ana fargabar sake kazancewar rikicin Libya bayan Turkiya ta yi barazanar daukar fansa kan duk wani hari da Khalifa Haftar ya kaddamar kan dakarunta.Haftar ya bayyana cewa, babu yadda za a samu zaman lafiya a Libya muddin dakarun kasahen ketare na ci gaba da kokarin mallake kasar. Wannan na zuwa ne a yayinda ake sa ran gudanar da zaben da zai kai ga samun sabon shugaban kasar a karshen shekara mai kamawa. Ko ya masana ke kallon wannan rikicin na Libya da ya ki ci ya ki cinyewa, Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattaunawa da Farfesa Kamilu Sani Fagge, masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero ta Kano.

Fargabar ta biyo bayan ikirarin Turkiya na mayar da martani kan Haftar muddin ya kaddamar da farmaki kan dakarunta.
Fargabar ta biyo bayan ikirarin Turkiya na mayar da martani kan Haftar muddin ya kaddamar da farmaki kan dakarunta. Getty Images
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.