Isa ga babban shafi
Afrika

An cinnawa gidan Bozize wuta

A Jamhuriyar Tsakiya Afrika, an cinnawa gidan tsohon Shugaban kasar Francois Bozize wuta yayinda suka rage kwanaki uku a gudanar da zaben shugabancin kasar.

Jami'an tsaro na gudanar da aikin tsaro a wata unguwar birnin Bangui
Jami'an tsaro na gudanar da aikin tsaro a wata unguwar birnin Bangui RFI/Charlotte Cosset
Talla

Hukumomin kasar na zargin tsohon Shugaban kasar Francois Bozize da rura rikicin siyasa tareda kulla yarjejeniya da kungiyoyin yan tawaye da nufin hana zabukan kasar na ranar 27 ga wannan watan da muke cikin sa .

Shugaban kasar kuma dan takara Faustin Archange Touadera ya sanar da yan kasar cewa babu abinda zai hana a gudanar da zabe a wannan kasa da aka share dogon lokaci kungiyoyin dauke da makamai ke cin karnen su ba babbaka.

Cinawa gidan tsohon Shugaban kasar wuta na saka jama’a cikin zulumi dangane da yiyuwar zaben shugaban kasar na ranar lahadi,inda dakarun majalisar dimkin duniya ke ci gaba da sintiri a wasu manyan tittunan babban birnin kasar Bangui.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.