Isa ga babban shafi
Afrika

Jami’an tsaro sun kubutar da dalibai 80 da aka sace a Najeriya

Jami’an tsaro a Katsina dake Najeriya sun ce sun yi nasarar kubutar da daliban makarantar Islamiyya kusan 100 da Yan bindiğa suka sace daren jiya asabar a Karamar Hukumar Dandume. Rahotanni sun ce Yan bindigar sun sace daliban ne akan hanyar su ta komawa gida bayan sun halarci bikin Maulidi a kauyen Unguwar Al-Kasim a daren jiya. 

Taswirar tarrayar Najeriya
Taswirar tarrayar Najeriya Wikipedia
Talla

Kakakin rundunar Yan Sandan Jihar Katsina Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar lamarın, inda yake cewa sun samu labarin sące daliban da misalin karfe 10 na dare, kuma nań take Baturen Yan Sandan Yankin ya jagoranci jami’an sa da na rundunar Sharan Daji da kungiyoyin sa kai inda suka fafata da Yan bindigar.

Isah yace jami’an tsaron sun yi nasarar kubutar da mutane 84 da Yan bindigar suka sace, cikin su harda daliban 80 da kumą kwato shanu 12 da Yan bindigar suka sace.

Kakakin Yan Sandan yace jami’an su na can suna bin sawun Yan bindigar domin kamą wadanda suka samu raunuka daga cikin su.

Sace wadanan dalibai na zuwa sa'o'i 48 da kubutar da daliban makarantar Kankara 344 da kuma  sace wasu tarin mutane da kungiyar Boko Haram ta yi awon gaba da su ranar juma'ar da ta gabata akan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.