Isa ga babban shafi

Kusan malaman makaranta 1500 ne Korona ta kashe a Afrika ta Kudu

Annobar COVID-19 ta yi wa bangaaren ilimi a Afrika ta Kudu mummunar duka, inda malamai har dubu 1 da dari 4 da 93 ne suka mutu sakamakon harbuwa da cutar, a cewar ministar ilimi a matakin farko ta kasar, Angie Motshega.

Ma'aikatan lafiya dake bada gudummawa a yaki da Korona a Afrika ta Kudu.
Ma'aikatan lafiya dake bada gudummawa a yaki da Korona a Afrika ta Kudu. Michele Spatari/AFP/Getty Images
Talla

Ministar ta ce jadawalin karatu na shekarar 2020 ya kasance da gagarumin kalubale sakamakon bullar annobar.

Ta shaida wa wani taron manema labarai cewa sun yi asarar dimbim ma’aikata da suka hada da manyan jami’an ilimi na yankuna da sauransu.

Sai dai ta ce duk da haka, shekarar ilimi ta 2021 za ta soma ne a ranar 25 ga watan Janairu, inda maalamai da dalibai za su koma ajizuwa a ranar 27 ga watan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.