Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu ya killace kansa saboda Coronaviru

Shugaban Afrika ta kudu Cyril Ramaophosa ya killace kansa, bayan gwaji ya gano wani da suka yi mu’amala tare na dauke da cutar Covid-19.

Shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu.
Shugaba Cyril Ramaphosa na Afrika ta kudu. Jerome Delay / POOL / AFP
Talla

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar yau Laraba, ta ce shugaban ya halarci taron cin abincin daren da gidauniyar Adopt-a-School ta shirya a Asabar din da ta gabata, wanda kuma bayan watsewa daga taron aka gano wasu na dauke da Covid-19.

Sanarwar ta ce zuwa yanzu shugaban bai fara ganin alamomin cutar ba, amma yana ci gaba da bin matakai da shawarwarin jami’an lafiya.

Taron wanda ya samu halartar manyan baki 35 galibinsu gwajin da suka gudanar a ranakun Lahadi da Litinin wadanda kuma sakamako ya fito a jiya Talata ya nuna cewa suna dauke da cutar Covid-19.

Rahotanni sun bayyana cewa taron ya gudana ne karkashin matakan kariya daga Covid-19 ta yadda aka bayar da tazara tsakanin jama’a kuma aka kauracewa musabaha da hannu haka zalika kowanne na sanye da mayanin rufe hanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.