Somalia ta harbe wasu masu wakiltar Al Shebaab wajen aikata kisa
Hukumomin Somalia sun harbe wani malamin makaranta tare da wasu mutane biyu a bainar jama’a saboda samun su da laifin kisa a madadin kungiyar Al Shebaab.
Wallafawa ranar:
Malamin Mohammed Haji Ahmed da ke koyar da Turanci a kwalejin Mogadishu na da hannu wajen kashe jami’an gwamnati da dama a madadin kungiyar Al Shebaab.
Rahotanni sun bayyana shi a matsayin mara Imani, wanda ya yi kaurin suna wajen aikata kisan ciki harda na Janar Abdullahi Mohammed Sheikh a shekarar 2017 da mataimakin babban lauyan gwamnati Mohammed Abdurrahman Mohammed a shekarar 2019 da kuma shugaban 'yan Sanda janar Mohammed Haji Alow.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu