Isa ga babban shafi
Wasanni

Tsohon gwarzon dan wasan Senegal Papa Diof ya rasu

Tsohon dan wasan tsakiya na kasar Senegal da Fulham da Portsmouth Papa Bouba Diop ya rasu yana da shekara 42, bayan dogon jinya.

Tsohon dan wasan Senegal Papa Bouba Diof
Tsohon dan wasan Senegal Papa Bouba Diof Reuters
Talla

Diop ya buga wasanni 129 a gasar Premier sannan kuma ya yi wasanni a Ingila tare da West Ham United da Kuma Birmingham City.

Marigayin ya buga wa Senegal wasa a gasar neman cin Kofin Duniya na shekarar 2002, inda ya ci kwallon a wasan farko na bude gasar da suka doke Faransa da ci daya mai ban haushi.

Hukumar Fifa jinjina masa ta shafukan sada zumunta, tana cewa, ya taba zama gwarzon gasar cin Kofin Duniya, kuma zai ci gabata zama gwarzo na har abada.

Club din Fulham ta nuna jimami ta shafinta na twitta.

Senegal ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin duniya ta 2002, inda Diop yaci kwallaye 3, ciki harda 2 da yaci a karawar da suka tashi 3-3 da Uruguay a wasan rukuni-rukuni.

Ya kuma taka rawar gani a wasannin cin Kofin Kasashen Afirka guda hudu, kafin Ya yi ritaya a shekarar 2013.

Diop ya taimakawa Portsmouth, karkashin jagorancin Harry Redknapp, inda suka dauki Kofin FA a 2008.

Shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya kira mutuwar Diop a matsayin "babban rashi ga Senegal" yayin da dan wasan tsakiyar Senegal da Liverpool Sadio Mane ya wallafa jimamin rashin a shafinsa na Instagram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.